Jam'iyyar adawa ta MRC a Kamaru ba ta shiga zabe
November 26, 2019A Kamaru jam'iyyar MRC Mouvement pour la Renaissance du Cameroun ta sanar da janye kanta daga zabukan kananan hukumomi da na majalisar dokoki da kasar za ta shirya ranar tara ga watan Febuwarin 2020. Jam'iyyar ta ce ta dauki wannan mataki ne sabili da rashin zaman lafiyar da ake fama da shi a yankunan da ke amfani da Turancin Inglishi.
Yayin wani taron manema labarai ne da ya kira a birnin Yaounde, shugaban jam'iyyar ta MRC Maurice Kamto wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na ranar bakwai ga watan Oktoban 2018 ne ya sanar da janye jam'iyyar tasa daga zabukan kananan hukumomi da na majalisar dokoki. Wannan sanarwar ta zo ne daidai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato ELECAM ta tsayar da daukan sunayen wadanda za su wakilci jam’iyyinsu a zabukan na tara ga watan Febuwarin 2020. Maurice Kamto ya bayyana dalilin janye MRC daga wadannan zabukan a gaban manema labarai inda ya ce:
"Bai dace ba a yi zabe yayin da wasu yankunan Kamaru ke cikin matsalar tashe-tashen hankula a Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma. Ya ce kamata ya yi a ba wa al’ummar yankunan biyu damar zaben wadanda za su wakilce su na zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi. Amma ana daukarsu tamkar ba 'yan Kamaru ba, al’amarin da ke ba su damar neman raba kasar".
Yan siyasa a Kamaru ba su ji dadin janyewar MRC ba, kasancewarta jam'iyya ta biyu bayan jam'iyya mai mulki ta CPDM. Rashin shiga wadannan zabukan masu zuwa cikas ne babba ga makomar dimukuradiyya a Kamaru da ma Afirka baki daya. Jam’iyyar SDF ta bakin shugaban matasa na yankin Bamenda ta nuna bacin ranta kan yadda Maurice Kamto yake neman kujeran shugaban kasa ba bisa ka’ida ba.
Karo na biyu da kenan da jam’iyyun adawa ke janye kansu daga zabe, hakan ya faru a shekarar 1997 yayin zaben shugaban kasa, inda ita SDF ta janye kanta bayan ta samu nasarar lashe zaben 'yan majalisar dokoki a shakarar 1992, al’amarin da ya bai wa shugaban Kamaru Paul Biya damar ci gaba da zama kan madafun ikon kasar yau tsawon shekararu 37 kenan.