1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Karuwar kanan yara masu gararamba

January 3, 2023

Jami'ai masu kare hakkin yara kanana sun yi gargadin cewa, karuwar yara da ke gararamba a tituna na iya janyo yin safarar yaran da fyade.

https://p.dw.com/p/4LhNX
Kamaru | Bamenda | Yara | talla | Tituna
Karuwar yara masu talla a kan titunan KamaruHoto: Jean Marie Ngong Song/DW

A tsakiyar birnin Bamenda da ke zama cibiyar kasuwanci a Kamaru, yawaitar yara da ke tallace-tallace a kan titi na kara haifar da damuwa. Birnin mai cike da hada-hadar kasuwancin muhimman kayayyaki, a baya-bayan nan yara wadanda shekarunsu na haihuwa ba su wuce 12 ba sun shiga kai komo na tallace-tallace da zama yan kayi na yi. Yaran sun buwayi 'yan kasuwa, jigilar talla a kan titi na bukatar sintiri da naci kuma yaran sun san da haka. Yawan yara da suke talla a Bamenda ya karu ne, saboda rufe makaranta da aka yi a watan Disamba. Su kansu yaran, suna sane da hadarin da ke tattare da abin da suke yi. Nsoso Josephine jami'ar kare rayauwar yara ce a Bamenda, tana daya daga cikin mutanen da suke damuwa da wannan hali da ke faruwa. Bakar wahala da rikicin yankin da ke magana da Turancin Ingilishi ya haifar da kuma tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki da ake fama da shi a Kamaru, wani karin dalili ne da ke sa yara gararamba suna tallace-tallace a tituna.