Kamaru: Kamto ya bayyana a gaban kotu
October 5, 2019A kasar Kamaru an gabatar a wannan Asabar da madugun 'yan adawar kasar Maurice Kamto a gaban kotun sojoji da ke birnin Yaounde wacce za ta bayyana matsayinta a kan matakin shugaba Paul Biya ta dakatar da tuhumar da ake yi wa wasu shugabannin adawar kasar.
A ranar Juma'a ne dai shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya mai shekaru 86 ya sanar da daukar matakin dakatar da duk tuhumar da ake yi wa wasu shugabannin adawar kasar da suka hada da na jam'iyyar MRC ta Maurice Kamto ba tare da bayyana ko matakin zai shafi shugaban jam'iyyar ta MRC ba.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa a jumulce mutane 102 ne da suka hada da mambobin jam'iyyar ta Maurice Kamto su 90 za su bayyana a wannan zama na musamman da kotun sojin ta birnin Yaounde ta soma a wannan Asabar inda daruruwan magoya bayan jam'iyyar ta MRC suka hallara tun da sanhin safiya.