1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani dan takara ya yi ikirarin lashe zabe a Kamaru

Salissou Boukari
October 8, 2018

Daya daga cikin manyan 'yan takarar neman shugabancin kasar Kamaru Maurice Kamto, ya yi ikirarin lashe zaben kasar da ya wakana na ranar Lahadi da suka fafata tare da 'yan taraka ciki har da shugaban Paul Biya.

https://p.dw.com/p/36BvM
Kamerun, Maurice Kamto
Maurice Kamto dan takarar neman shugabancin kasar Kamaru da ya yi ikirarin lashe zaben kasarHoto: AFP/Getty Images

Dan takara Kamto ya yi wannan ikirari ne yayin wani taron manema labarai da ya kira, inda ya ce kamar a wasan kwallo ne ya samu bugon daga kai sai mai tsaron gida, kuma ya buga kwallo ya shiga. Dan takarar mai shekaru 64 da haihuwa, wanda tsohon ministan shari'a ne, kuma Lauya Maurice Kamto, shi ne shugaban jam'iyyar MRC ta "Mouvement pour la renaissance du Cameroun" ya ce ya samu  goyon baya daga al'umma wanda babu wani konkonto a cikinsa, kuma zai yi kokarin kare wannan nasara da ya samu. Dan takarar da ya yi ikirarin lashe zaben, ya ce ya na mai kiran bangaran na gwamnati da su bada kai domin suyi aikin kasa.