Mulkin takalmin kaza a Kamaru
October 22, 2018Shugaban dan shekaru 86 zai ci gaba da zama a karagar mulki har sai shekarar 2025 lokacin da zai kai shekaru 93 da haihuwa. Clement Atangana shugaban kotun tsarin mulkin kasar ta Kamaru ne ya bayyana sakamakon zaben. Shugaba Biya dai shi ya kwashe sama da kaso 70 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda Maurice Kamto na jam'iyyar Cameroon Renaissance Movement ya zamo na biyu kana Cabral Libii na Universe ya zamo na uku shi kuwa Joshua Osih na Social Democratic Front ya zamo na hudu. Dion Ngute, na kusa da shugaba Biya ne kana minista, ya bayyana cewa bai yi mamaki ba da sakamakon, kasancewar al'ummar Kamaru na gamsuwa da aikin Biya kuma suna son kari.
Martanin 'yan adawa
Joshua Osih na jam'iyyar adawa ta Social Democratic Front wanda kuma ya zamo na hudu a zaben ya ce bai amince da sakamakon zaben ba. Kotun tsarin mulkin kasar ta Kamaru dai a makon da ya gabata ta yi watsi da korafe-korafe 17 da 'yan adawar da suka hadar da Maurice Kamto da Cabral Libii da Osih Joshua suka gabatar, inda suka nemi a soke zaben na ranar bakwai ga watan Oktoban da muke ciki. Maurice Kamto da Cabral Libii sun bukaci 'yan Kamaru su tashi su kare hakkinsu idan ba su gamsu da sakamakon zaben ba. Wasu masu adawa da Biya dai na ganin ya kamata shi da kansa shugaban na Kamaru ya sani cewa ba shi ne ya yi nasara ba. Shugaba Paul Biya dai na mulkin kasar ta Kamaru tun daga watan Nuwambar shekara ta 1982 kuma ya kasance shugaban kasa mafi dadewa a kan karagar mulki bayan makocinsa Theodoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea. A shekarar 2008 ya sauya kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1996 inda aka cire wa'adi da shugaban kasa zai iya mulki, abin da ya bashi dama ya shiga zabe ya yi nasara a shekarar 2011.