Jamus: Mayar da kayan tarihin Kamaru
July 12, 2022Mutum-mutumin Lefem na daya daga cikin daruruwan kayan tarihin Afrika da ke Tarayyar Jamus, inda ake ajiye da shi a daya daga cikin gidajen tarihin birnin Cologne. Ya kasance gunki mai muhimmanci a wurin mutanen Bangwa da ke yammacin kasar Kamaru, wanda Jamus ta sace shekaru 120 da suka gabata a lokacin mulkin mallaka. Bayan an dauki lokaci ana kai ruwa rana, a makon da ya gabata gwamnatin Jamus ta bai wa tawagar masarautar ta Bangwa daga Kamaru damar zuwa kasar domin a tattauna batun mayar da mutum-mutumin zuwa kasar shi ta gado. Tawagar sarkin na Bangwa ta nuna jin dadinta, bayan ganin mutum-mutumin da suka jima suna jin tarihinsa a wurin kakanninsu.
Rashin wannan gunki a wurin mutanen Bangwa ba karamin koma baya ba ne, domin sun yarda cewar dawo da shi gida ne kadai zai bai wa kakanin-kakaninsu kwanciyar hankali a kaburburansu kuma ya kawo musu karshen matsalolin da suke fuskanta tun bayan batan gunkin kamar rashin tsaro da rsahin ci-gaba. Duk da wannan sarkin da mutanensa sun bayyana wa Jamus irin muhimmancin wannan gunki a wurinsu, wanda har ya saka su kuka da su da masu kula da gidan tarihin. Duk da irin halin da mutanen Bangwa suka tsinci kansu tun bayan sace gunkin Lefem, sun tabbatar da cewa ba su dora alhakin wahalar da suka sha a kan Jamus ba. Saidai sun yi fatan gwamnati za ta yi gaggawar dawo musu da mutum-mutuminsu domin su samu kwanciyar hankalin da suka rasa shekaru 120 da suka wuce.