Kamaru: Sojoji sun yi wa garin Buea kawanya
October 2, 2017Daya daga cikin mutanen da suka fito daga wannan yanki na Kamaru da ake magana da harshen Ingilishi shi ne jaroran 'yan adawa na kasar John Fru Ndi, wanda kuma ya yi hira da wannan tasha ta DW wanda ya ce hukumomin Kamarun sun yi watsi da yankin. John Fru Ndi shugaban jam'iyyar SDF kana jagoran 'yan adawa na Kamaru wanda ya fito daga yankin da ake magana da harshen Ingilishi ya danganta matsalolin da ake ciki da yadda shugaba Paul Biya na kasar ta Kamaru ke nuna ko'in kula game da matsalolin da kasar ke ciki, kuma ga abin da Fru Ndi yake cewa bisa wannan riciki a yankin da ake magana da harshen na Ingilishi."Matsalolin yankin da ake magana da harshen Ingilishi shugaba Biya ya kirkiro kuma ya aiwatar, saboda matsalolin da suke Kamaru shi Paul Biya ba ya duba su ko kadan. Lokacin da rikicin ya barke na ga yara kananan da suka shiga, sai na samu shugaba Biya na shaida masa cewa ya kamata ya yi wani abu domin lamarin ya wuce yadda aka saba gani,na shaida wa Biya wannan hadari ga kasa, amma bai kula ba." Wani salon gwagwarmayar da yankin ya dauka shi ne neman aware domin dara Kamaru gida biyu, kamar yadda 'yan gwagwarmayar masu magana da harshen Ingilishi ke bukata, wanda kuma bisa ga dukkan alamun John Fru Ndi bai nuna kin amincewa ba da haka.