Tsarin bunkasa Arewa maso yammacin Kamaru
July 3, 2018Talla
Wannan yankin dai na Arewa maso yammacin kasar ta Kamaru wanda ke fama da matsalar tashe-tashen hankulla na 'yan aware.
Kafofin yada labaran kasar ta kamaru ne dai suka sanar da wannan labari a wannan talatar.
A birnin Douala ma da ke a matsayin cibiyar kasuwancin kasar ta Kamaru, jama'a sun tattara kudade miliyan 229,4 na CFA a ranar Litinin da ta gabata, sannan kuma a karshen watan Yuni da ya gabata an samu tattara sama da miliyan 152 na CFA domin ayyukan gaggawa na bunkasa yankin da ake magana da turancin Ingilishi na kasar ta Kamaru, kamar yadda gwamnatin ta sanar a tsakiyar watan na Yuni cewa ta shirya wani tsari na gaggawa na bunkasa yankin.