1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen 'yan adawa a Zimbabuwe

Yusuf Bala Nayaya
January 16, 2019

'Yan sanda dauke da manyan bindigogi kirar AK47 sun kama Evan Mawarire, dan fafutika kuma malamin majami'a a gidansa da ke birnin Harare a wannan rana ta Laraba.

https://p.dw.com/p/3BfUc
Simbabwe Evan Mawarire Pastor Aktivist
Evan Mawarire malamin majami'a dan fafutukaHoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Wannan kamu dai lamari ne da ke zuwa yayin da gwamnati ke dauki dai-dai kan masu zanga-zanga a kasar saboda mara bayansu ga shirin zanga-zangar da ta biyo tsadar rayuwa da farashin mai a kasar ta Zimbabuwe.

Mawarire, a shekarar 2016 ya hada wani gangami na adawa da gwamnati abin da ya karade fadin kasar ta Zimbabuwe saboda abin da ya kira almubazzaranci da gwamnati ke yi da dukiyar al'umma da tsawon lokaci da Robert Mugabe da ke zama tsohon shugaban kasar ta Zimbabuwe ya yi a karagar mulki kafin daga bisani aka sauke shi.

To ko me ya sa aka kama wani malamin majami'a kuma dan fafutka fitacce a kasar ta Zimbabuwe yanzu? Beatrice Mtetwa ita ce lauya da ke kare  Mawarire ta ce an garzaya da shi ofishin 'yan sanda amma sun nemi jin dalilin kamun ya gagara.