1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamun ludayin Barack Obama a rikicin Yukren

Klaus JansenMarch 5, 2014

Shugaban Obama na Amirka fuskantar kalubalen dipolamasiya bayan kutsen da sojojin Rasha suka yi a tsibirin Krimieya na kasar Ukraine, sakamakon rashin bayyana matakin da zai dauka a kan Vladimir Putin.

https://p.dw.com/p/1BKe1
Hoto: picture-alliance/dpa

Ko shakka babu, takun saka da Rasha ta ke yi da kasashen yamma a kan tsibirin Krimeya ya zame wa Barack Obama kadangaren bakin tulu. Dalili kuwa shi ne ana ganin cewa ba shi da hanzarin yanke hukunci da ya dace a game da al'amuran da suka shafi rikicin kasa da kasa. Ko da a rikicin kasar Syriya da ma dai na Iran da manyan kasashen duniya, shugaban na Amirka ya yi ta cizo ya na hurewa, a inda a karshe ya fifita hanyoyin siyasa maimakon daukan mataki na soje.

Obama na shan suka daga 'yan Republicans

Senatar John Mccain na jam'iyyar Republican na ganin cewa Obama ba shi da alkibla a al'amuran da suka shfi manufofin harkokin waje. Maimakon haka ma dai a cewarsa shugaban na Amirka ya na mika kai bori ya hau a duk wasu al'amuran da suka kunno kai tsakanin Amirka da Rasha. Maccain ya yi misali da rikicin nukiliyar Iran da kuma na Syriya, inda ya ce a karshe Obama ya kasa nuna wa Rasha 'yar yatsa duk kuma da ruwa da tsaki da ta ke da yi a rikice-rikicen kasashen biyu. Hakazalika Vladimir Putin ya bai wa tsohon dan leken asirin Amirka Edward Snowden mafaka na wani lokaci, duk da nemansa ruwa a jallo da hukumomin Washington ke yi bayan da ya kwarmato wasu bayanan sirri.

G8-Treffen
Da kamar wuya Obama ya halarci taron G8 da Putin zai shirya a RashaHoto: Reuters

Neman kare Obama daga zargin gazawa

Tsohon jakadan Amirka a kasar Poland Lee Andrew Feinstein ya kare Barack Obama inda ya ce "Shugaba Obama da kuma sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry sun yi kakkausar suka bayan da Rasha ta yi wannan tsokanar fada. Kerry ya danganta wannan mataki da shiga shara ba shanu, yayin da Obama ya kirashi keta dokokn kasa da kasa. Kwana daya bayan haka ne kasashen Turai suka bi sahunsu wajen yin Allah wadai da matakin na Rasha. Dole ne a bar wa Putin kofa a bude, domin bashi damar lashe amansa idan bukata ta taso."

Manufar Obama game da rikicin Yukren

Shi dai Obama ya yi barazanar daukan matakai a kan takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin idan ya ki janye dakarunsa daga tsibirin Krimeya mallakar kasar Yukren. Tuni ma dai gwamnatinsa ta yi shirin kakaba wa hukumomin Moscow jerin takunkuman karya tattalin arziki. Dadin dadawa ma dai Amirka ta janye kanta daga shirye-shiryen taron G8 da birnin Sotchi na Rasha ya kamata ya dauki bakwancinsa.

Obama na daukan wannan matakin ne da nufin mayar da Rasha saniyar ware a duniya. Sannan kuma shugaban na Amirka ya tura da sakataren harkokin wajensa Kiev babban birnin Yukren, tare da alkawarin taimaka ma wannan kasa da kudi domin ta tayar da komadar tattalin arzikinta da ke cikin wani mawuyacin hali. A takaicen takaicewa dai, Obama na matsa wa Rasha lamba a fannonin siyasa da kuma na tattalin arziki, yayin da a daya hannun kuma ya ke taimaka wa Yukren tsayawa a kan kafafunta.

Georgien Russland Krieg 2008
A rikicin Georgia a 2008 ma, an yi takun-saka tsakanin Amirka da RashaHoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Kiran Obama ga daukan matakin soje

Sai dai tsohon jakadan Amirka a Jamus John Kornblum ya ce kamata ya yi Obama ya nuna wa Putin na Rasha gajiyawarsa. Ya ce "Muhimmancisa wannan mataki shi ne kare martabar kasa. Amma idan ku ka ce mene ne amfanin wannan? ma'ana ba a bukatan matakin soje ke nan. Amma kuma zai zama wani kwakwaran mataki na siyasa da kuma na tattalin arziki."

Babban matakin da Obama ke da niyan dauka idan rikicin tsibirin Krimiya ya dauki wani sabon salo, shi ne haramta wa kusoshin gwamnatin Rasha taba kudadensu na ajiya a bankunan kasashen yamma. Sai dai ya na bukatan hada guywa da kasashen Turai domin kwalliyarsa ta mayar da kudin sabulu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar