Iran ta kare kanta game da rikitowar jirgin Ukraine
January 8, 2020Sanarwar ta kara da bayyana yadda samun cikakkun bayanai daga kasar Iran zai yi wahala sakamakon rufe ofishin jakadanci da Kanada ta yi a kasar ta Iran da kuma dakatar da harkokin jakadanci tun shekara ta 2012. Jirgin saman kasar ta Ukraine dai ya rikito ne mintuna kalilan bayan Iran ta harba makamai masu linzami a sansanin sojin Amirka dake Iraki da nufin daukar fansar mutuwar Janar Kassim Soliemani, kodayake mahukunta kasar ta Iran sun bayyana tangardar na'ura daga jirgin na Ukraine a matsayin abinda ya haifar da fadowar jirgin mai dauke da daliban kasashen ketare da kuma wasu iyalai.
Lokacin da yake hakurkurtar da iyalan wadanda ibtila'in ya rutsa dasu ministan sufurin kasar ta Kanada Marc Garneau ya jaddada aniyar gwamnati ta shiga a dama da ita cikin binciken da kasar Iran zata fuskanta.