1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada ta karbi rukunin farko na 'yan Siriya

Gazali Abdou TasawaDecember 11, 2015

'Yan Siriya 163 akasari mata da kananan yara daga kasashen Jodan Lebanan da Turkiya sun isa a birnin Toronto inda suka samu tarba daga Firaminista Justin Trudeau na kasar ta Kanada.

https://p.dw.com/p/1HLfY
Syrische Flüchtlinge kommen in Kanada an Justin Trudeau
Hoto: Reuters/M. Blinch

Jirgin farko na 'yan gudun hijirar Siriya ya isa a cikin daran jiya washe garin wannan Jumma'a a kasar Kanada. Jirgin wanda ya taso daga birnin Beyrouth dauke da 'yan Siriyar 163 akasarinsu mata da kananan yara ya yada zango a kasar Jamus kafin ya sabka a filin jiragen sama na birnin Toronto .

Firaministan kasar ta Kanada Justin Trudeau wanda ya tarbi bakin da kansa ya bayyana wannan rana a matsayin wace tarihin kasar ba zai taba mantawa ba. Kasar Kanada dai ta kasance kasar yankin Amirka ta Arewa ta farko da ta bayar da mafaka ga 'yan gudun hijirar kasar ta Siriya.

Gwamnatin Justin Trudeau ta yi alkawarin karbar 'yan gudun hijirar kasar ta Siriya dubu 25 daga kasashen Jodan da Labanan da Turkiyya zuwa karshen wannan wata na Disamba kafin daga bisani ta rage adadin zuwa dubu 10 biyo bayan harin birnin Paris na ranar 13 ga wtan Novambar da ya gabata.