Kano: Tallafawa marasa lafiya
November 22, 2017
Daruruwan mutane ne suka hallara a kofar hidan Alhaji Sule Na’abba a dogon lungu, a ranakun Asabar da Lahadi don a binciki cututtukan da suke fama da su a kuma basu magunguna kyauta a cewar Mal Abubakar Na’abba jagoran shirin kula da lafiyar al’umma da kungiyarsu ta kirkira.
"Ko ina mutum ya zo idan dai ba ka da lafiya za a duba ka abin da ya sameka kama daga harkar da ta fi shafar Malaria hawan jini Typhoid da kuma sanyi da ya fara shigowa dinnan, ciwon sugar akwai abin da za mu ce har da shi ba, shi ma ana dubawa sai a ba su shawarwari su tafi asibiti lokaci kaza. To wannan a kan tsarin ake kuma har ya zuwa yanzun nan da muke aikin abin ya ninka ma na jiya."
Duk da cewa Gwamnatin Kano ba ta gaza ba ta bangaren kula da lafiyar, amma a cewar Malam Abubakar hannu da yawa ne zai iya maganin kazamar miya.
"Idan dai za' a tsaya a taimaka a dubi al’umma wallahi gwamnati ma babu ruwanmu da ita.A junanmu ma za mu iya zama gwamnati mu tsara al’ummarmu al’amuran da zasu ji dadi. Domin wannan ya nuna mana danba domin ko yanzu said a wani likita ya gaya mana tuni har sun fara shirin wata unguwa zasu yi irin wannan tsarin namu da muka yi".