1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karamba Diaby dan Afirka a majalisar Jamus ta Bundestag

September 18, 2013

A karon farko, dan asalin Afirka ya sami nasarar shiga majalisar dokokin tarayyar Jamus wato Bundestag bayan zabe a ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/19k2g
Hoto: picture-alliance/dpa

Karamba Diaby ya shiga takara a madadin jam'iyar Social Democrats wato SPD a yankin Halle, lokacin zaben majalisar dokokin tarayya ranar Lahadi da ta gabata, kuma ya sami nasarar kasancewa dan majalisar dokokin Jamus na farko dan asalin Afirka a majalisar ta Bundestag. Lokacin kampe ya bi gida-gida domin saduwa da masu kada kuri'u inda ya nemi goyon bayansu.

Ko za ka karbi takardar bayani game dani kan zaben majalisar dokokin tarayya dake tafe nan gaba kadan?

Karamba Diaby mutum ne da ya san abin da yake so da yadda zai kai gareshi. A garin Halle dake yankin gabashin Jamus, yana da wuya mutum ya ci karo dashi, ya wuce bai saurare shi ba. A hanunsa, Diaby dan shekaru 52, yana rike da jakarsa. A duk inda yake, yakan nemi musabaha da masu sauraronsa, yakan so yin ba'a dasu, da neman kusantarsu. Yanzu haka yana cikin hali na kampe, saboda neman zama dan majalisar dokokin Jamus a madadin jam'iyar SPD a matsayin na farko dake da tushensa daga Afirka.

Ina ganin yana da kyau idan mutum yazo domin kawai ya gaida mutane.

Diaby yakan ziyarci masu kada kuri'u har gida, ya buga masu kofa, ko ya kada masu kararrawa, ko ya nemi hira da mutane dake tsaye ko suna aiki a lambunansu, ya mika masu hannu domin musabaha, domin jan hankalinsu, adda idan aka zo zaben na ataraiya, mazauna garin Halle zasu kada kuri'unsu a kan sunansa.

Tür zu Tür Wahlkampf mit Karamba Diaby
Karamba Diaby yana bi gida-gida yana kampe....Hoto: Christoph Richter

Diaby yana da kyakkyawar dama ta samun nasarar shiga majalisar dokokin tarayya ta Bundestag. Manufofin da ya ke maida hankali kansu, sun hada har da ilimi da cudanyar baki da biyan ma'aikata albashi mafi dacewa da kuma halin zaman tare a yankin gabashin Jamus, tun bayan faduwar katangar Berlin da rushewa ko bacewra masana'antu a yankin tun bayan sake hadewar Jamus, abin da ya kawo asarar aiyukan yi ga mazauna yankin masu yawan gaske. Hakan ya sanya da yawa suna daukar kansu a matsayin wadanda suka yi asara ko wadanda suka tura mota amma ta tafi ta bade su da hayaki. Irin wadanan mutane ne Diaby yace zai basu murya, wato zai wakilci bukatunsu a majalisar dokoki. Zai yi amfani da kwarewarsa a wannan fanni domin cimma nasara.

Yace surukata tayi aiki a Buna a matsayin mai tuka injin wurin aikin gini. Bayan rushewar katangar Berlin da hadewar Jamus aka rufe kamfanin da tayi wa aiki. Ta kasance mata ce mai kwazo da 'ya'yanta biyu da ita ta rene u har suka girma. Daga baya tace ba zan zauna a gida kawai ba duk da asarar wurin aikina.

Maimakon haka sai ta sake samun horo a matsayin mai kula da masu fama da nakasa, ta kuma tashi daga garin da take na Merseburg zuwa arewacin yankin Franken. Tasha wahala matuka har lokacin mutuwarta tana da shekaru 59 kawai a duniya.

Yayin da wasu yan siyasa suke ta yawo da manyan motoci na alfarma suna kampe, Karamba Diaby ya gwammace ya hau kekensa da aka kera a gabashin Jamus a jihar Saxony. Stefan Will, abokinsa kuma magoyin bayasa yace:

Yadda yake kusantar jama'a, ba tare da toro ko kyama ba abin alfahari ne garemu gaba daya. Ina nufin dole ne mutum ya dubi asalin sa a matsayin bako da ya fito daga Afirka. Duk da haka, yana kusanci mutane gaba-gadi kai tsaye, kuma baya bari a kaskantar dashi kawai ya zua ga jinsinsa ko asalinsa.

Tür zu Tür Wahlkampf mit Karamba Diaby
....a kan kekensa kirar gabashin JamusHoto: Christoph Richter

A bayan faduwra katangar Berlin, Diaby yaci gaba da zama a gabashin Jamus, inda a shekarata 2001 ya zama Bajamushe. A shekara ta 1986 ya bar kasarsa ta asali zuwa Jamus ta gabas saboda ya hangi kyakkyawar dama a wannan kasa. Duk da iliminsa mai zurfi da al'amuransa na siyasa, amma Diaby har yanzu yana nan da damuwar makomar masu karamin karfi. Musamman a yankin gabashin Jamus, inji shi, ba sosai a kan bai wa jama'a damar ba da gudummuwarsu ga al'amuran da suka shafi makomarsu ba.

Mawallafi: Christoph Richter / Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman