Kalubalen abinci mai gina jiki
November 29, 2018Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniyar FAO ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na shekara, inda ta ce duniya na fuskantar barazana sakamakon yadda yunwa ke ci gaba da karuwa, wanda ta ce lamarin bai bar kasashe masu karfin tattalin arziki ba balle mataalauta. Hukumar ta ce kasashen duniya na fama da ko dai rashin abinci mai gina jiki a cikin kasashe matalauta ko kuma matsalar kiba a cikin kasashe masu karfin tattalin arziki. Rahoton na FAO da aka yi wa taken: "Global Nutrition Report", ya shafi kusan kasashe 200.
Farfesa Ashiru Garba kwararren likitan yara ne da ke Tarayyar Najeriya wanda kuma ke bincike kan matsalar yunwa da ke addabar kananan yara, a wata hira da ya yi da tashar DW ya alakanta wannan matsalar batun sauyin yanayi da ke addabar duniya baki daya. Karkashin tsarin muradun ci-gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya wato Sustainable Development Goals, za a yi kokarin kawar da yunwa nan da shekara ta 2025. Matsalar yunwa dai ta kasance babban abin da ke lakume rayuka a kasashe masu tasowa musamman na yara kanan da mata masu juna biyu, wadanda ke mutuwa sakamakon rashin abinci mai gina jiki.