Matsalar wutar lantarki a Ghana
April 3, 2024Rashin wutar ya ma haddasa mutuwar wani jariri a asibitin garin Tema a makon da ya gabata. To sai dai hukumar lantarki ta kasar ta daura laifin abunda ke faruwa kan lodin da akeyi wa taransufomomin da ke bada wutar. A yayin da duhu ke kawo kai, wutar kendir na taimakawa Rakiya Mumuni da ke birnin Tamale wajen girka abinci.
Matsalar lantarki matasalace da ta shafi kusa dukkan wani al'amari ba kawai na harkokin cikin gida irin wadanda rakiya ke yi ba. A gefen titin yankin Kanvili, rashin wuta ya mayarda masu aikin walda 'yan zaman kashe wando. 'Yan kasuwa ne dai ke samar da kaso da yawa na wutar lantarki a Ghana kuma suna bin gwamnatin kasar kudin wuta dala biliyan 1.7.
Kasar ta Ghana da Allah ya horewa albarkatun kasa dai na neman komawa gidan jiya musamman a shekarun 2013 zuwa 2015 lokacin da kasar ta fuskanci gagarumin daukewar lantarki. Bayan dan sararawa na kusan shekara 10, kasar na neman sake tsunduma cikin duhu laifin da da daama ke daurawa kan rashin shugabanci na gari.
A makon da ya gabata wani jariri ya mutu a asibitin Tema saboda rashin wutar lamarin da ya 'yan kasar ta Ghana da dama suka bayyana a matsayin abin takaici.
Ghana dai ita ce kasa ta 7 mafi tsadar wutar lantarki a cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka. A yayin da wutar ke da tsada ga masu karamin karfi, babu ma tabbas kan samunta kamar yadda ya dace. To sai dai kuma fa gwamnati kam ta ce ta magance matsalar a nata bangaren kuma duk wadanda wutarsu ke ci gaba da yin dillin dillin to wata matsalace ta yankunansu ba daga gareta ba.