Karancin yara da ke zuwa makarantu a Najeriya
June 16, 2014Yayinda ake bukin ranar yarar nahiyar Afirka, Aususun kula da ilimin yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya bayyana cewa matsalar tasaro ya haifar da gagarumar matsalar ga ilimin yara, musamman ‘yan mata a yankin Arewacin Najeriya.
Taken bukin tunawa da ranar yaran Afirka na bana dai, shine samar da ingantaccen ilimi kyauta. Kwararren jami'in sadarwa na Asusun UNICEF a Najeriya Geoffrey Njoku ya bayyana a wata sanarwa da Asusun ya fitar cewa, taken dama ce ta yin dubiya ga yanayin da ilimin yara ya shiga a Najeriya.
Sanarwar da Asusun ya fitar, ta nuna cewa a Tarayyar Najeriya akwai kimanin yara miliayan daya da budu dari (10.1 milion) da suka bar makaranta inda kimanin kashi 60 cikin dari, na wadan nan yara mata ne daga yankin Arwacin Najeriya.
Masana ilimi ma sun bayyana damuwa da wannan alkaluma, inda suke ganin akwai yiwuwar karuwar yawan dalibai da za su kauracewa makarantunsu, saboda yadda matsalolin tsaron ke kara tabarbarewar. A cewar Malam Ahmad Gire rashin magance matsalar tsaron wanda ke haifar da koma baya a harkokin Ilimi a yankin Arewacin kasar, wata aba ce da yan siyasa suka haddasa.
Wannan ma kuma shine ra'ayoyin wasu iyayen da suke zargin gwamnatin Tarayyar kasar da kasa sauke hakkokin da ke kanta, na kare rayuka al'ummar da ta sha rantsuwar karewa.
Mawallafi: Al-Amin Suleiman Mohammed
Edita: Usman Shehu Usman