Takun saka kan kundin tsarin mulki
April 25, 2024Jam'iyyu adawa na kasar Togo da ke yankin yamamcin Afirka sun shigar koke a kotu game da yunkurin shigar da gyara ga kundin tsarin mulki da zai bai wa Shugaba Faure Gnassingbe damar fadada wa'adin mulkinsa.
Kungiyoyin fararen hula da jam'iyyun siyasa 13 suka shigar da karar a gaban kutun kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, inda suke zargin gwamnatin ta Togo da karya ka'idodjin tsarin dimukaradiyya na kasar.
Gyare-gyaren kundin tsarin mulkin da majalisar dokokin wannan karamar kasa ta amince, sun kunshi mayar da kasar daga tsarin zaben shugaban kasa kai tsaye zuwa yadda majalisar dokoki za ta zabi shugaban kasa. 'Yan adawa suna zargin majalisar dokokin ba ta da hurumi, saboda wa'adin majalisar ya kare yayin da aka jinkirta zabe.
Tun shekara ta 2005 Faure Gnassingbe yake kan madafun ikon kasar ta Togo inda ya gaji mahaifinsa wanda shi ma ya shafe kimanin shekaru 40 yana mulkin kasar.