1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa dangantaka tsakanin China da Switzerland

Abdullahi Tanko Bala
January 15, 2024

China da Switzerland sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta karfafa dangantaka a tsakaninsu bayan da Firimiya Li Qiang ya gana da shugaban kasar Switzerland

https://p.dw.com/p/4bHWf
Shugabar Switzerland Viola Amherd da Firaministan China Li Qiang
Shugabar Switzerland Viola Amherd da Firaministan China Li QiangHoto: Peter Klaunzer/REUTERS

Li wanda shi ne jami'i mafi girman mukami na China da ya kai ziyara Switzerland tun bayan ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai a 2017, ya gana da shugabar Viola Amherd tare da tawagar manyan jami'an China gabanin babban taron tattalin arziki na duniya a Davos.

Yarjejeniyar hadin gwiwar za ta karfafa kasuwanci ba tare da shinge ba a tsakanin kasashen biyu wanda ake gani babban mataki na share fagen karin tattaunawa a tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

China dai ita ce babbar kasa ta uku abokiyar cinikayya da Switzerland bayan Amurka da kungiyar tarayyar Turai.