1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomi Iran sun bukaci zama a gida

Abdoulaye Mamane Amadou ZMA
March 15, 2020

Hukumomin Iran sun yi kira ga jama'a da su dakata a gidajensu sakamakon karuwar yaduwar annobar Corona kamar wutar daji a kasar.

https://p.dw.com/p/3ZSlg
Iran Coronavirus
Hoto: picture-alliance/AA/F. Bahrami

Hukumomi Iran sun yi kira ga 'yan kasar da su kasance a gida domin rage radadin yaduwar cutar Coronavirus a daidai lokacin da annobar ke ci ga hallaka rayukan wadanda suka kamu da ita kasar.

Ko a yau Lahadi kakkain ma'aikatar lafiyar kasar ya tabbatar da karin mamata 113 bayan da aka gano sun kamu da cutar ta Covid-19, alkaluman da suka kara adadin wadanda suka mutu zuwa 724, wanda kuma hakan ya jefa kasar ta Iran daga cikin na kan gaba a jerin kasashen da ke fama da cutar a duniya.

Tuni dai ma'aikatar lafiyar kasar ta yi kira ga jama'a da ma wadanda za su balaguro da su dakata a gidajensu takuna har sai lokacin da kura ta lafa.