1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na ci gaba da tururuwa zuwa Turai

Suleiman Babayo / LMJSeptember 7, 2015

'Yan gudun hijira da suka samu shiga nahiyar Turai na ci gaba da tururuwar kai wa ga kasar Jamus, inda suke fatan samun kyautatuwar rayuwa.

https://p.dw.com/p/1GSSF
'Yan gudun hijira da tarbar da suka samu a Jamus
Hoto: Reuters/M. Rehle

Dubban 'yan gudun hijirar galibi na shiga kasar ta Jamus ta jihar Bavariya, wasu da jiragen kasa wasu kuma a motoci yayin da wasu ke takawa da kafa bayan ficewa daga kasar Hangari. Masu fafutukar kare hakkin dan Adam daga kasashen Ostiriya da Jamus sun yi amfani da motocinsu wajen taimakon 'yan gudun hijirar. Wasu daga cikin 'yan gudun hjirar da suka samu shiga Jamus sun nuna farin ciki kamar yadda wannan mutumin daga yankin Kurdawa ke cewa:

Godiya ga Jamusawa

"Mun gode wa Jamus matuka. Jamusawa sun yi mana kyakkyawar tarba da zuciya daya mun yi musu godiya daga cikin zuciyarmu."

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da batun 'yan gudun hijira
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da batun 'yan gudun hijiraHoto: AFP/Getty Images/T. Schwarz

Manyan jami'an gwamnatin hadaka ta kasar ta Jamus sun amince da ware kimanin Euro milyan 6,000 domin kula da 'yan gudun hijirar. Euro milyan 3,000 yana cikin kasafin kudin shekara ta 2016, yayin da sauran miliyan 3,000 za a yi amfani da su wajen taimaka wa jihohi da kananan hukumomi. Ga dai abin da wata Bajamushiya daga cikin masu tarbar bakin haure da 'yan gudun hijira ke cewa:

"Idan zan yi gudun hijira zan je kasar da za a yi maraba da ni, ba inda ba a kaunar baki ba."

Wani taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar Tarayyar Turai da ya gudana a karshen mako a Luxembourg ya gaza amincewa da hanyoyin magance matsalolin masu kwarara zuwa nahiyar ta Turai. Babbar jami'ar kula da harkokin kasashen ketere ta kungiyar Federica Mogherini ta ce yayin da kasashen na Turai ke cece-kuce a kan 'yan gudun hijira 1,000, ko 10,000 ko 42,000 ko ma 100,000 kasa za ta iya dauka, tuni kasa kamar Turkiya ta karbi milyan biyu.

Lokaci ne na hadin kai

Mogherini ta kara da cewa lokaci ya yi da kasashen Turai za su fuskanci zahirin abin da ke faruwa:

Taron ministocin kasashen waje na EU a Luxemburg kan batun bakin haure
Taron ministocin kasashen waje na EU a Luxemburg kan batun bakin haureHoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

"Mu kara karfin hadin kan aiki tare ba kokarin dora laifi ga wani ba, duk muna fuskantar wani mawuyacin yanayi. Ba zan kira shi da yanayi na gaggawa ba, domin abu ne na dogon lokaci, kuma da zarar mun amince da haka a hankalce da kuma a siyasance, za mu gano hanyar warware matsalar cikin sauki."

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya nemi iyalai mabiya darikar a kasashen Turai da su dauki dawainiyar 'yan gudun hijira. Tuni fadar ta Vatican ta ba da misali. Kasar Ostiriya ta fara tunanin kawo karshen matakin gaggawa da ta dauka wanda ya janyo dubban 'yan gudun hjira suka samu shiga kasar ba tare da wasu takardu ba daga kasashen Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, bayan samun gawarwakin 'yan gudun hijira fiye da 70 a cikin wata motar daukar kaya da kuma gano gawar karamin yaro dan kasar Siriya a bakin gabar ruwan kasar Turkiya. Shugaban gwamnatin Ostiriya Werner Faymann ya ce sun dauki matakin bisa dalilai na jinkai bayan tattaunawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma Firaminista Viktpor Orban na kasar Hangari.