1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin kwararar bakin haure a tsibirin Mellila na kasar Spain

May 28, 2014

Tun farkon wannan shekara yawan bakin haure 'yan gudun hijira da suka samu nasarar shiga yankunan kasar Spain na Melilla da Ceuta ya karu.

https://p.dw.com/p/1C8VI
Melilla Zaun Flüchtlinge 28.05.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan gudun hijirar Afirka sun sake yin dirar mikiya a kan tsibirin Melilla da ke zama mallakin Spain da ke yankin arewacin Afirka. Shugaban birnin Melilla Juan Jose Imbroda ya fada wa gidan rediyon Spain RNE cewa daga cikin 'yan gudun hijira fiye da dubu daya, kimanin 400 sun samu nasarar tsallaka kan iyaka mai cikakken tsaro daga Marokko zuwa yankin da ke zama wani yanki na tarayyar Turai. Wannan dai shi ne adadi mafi yawa da aka samu tun shekarar 2005. Tun farkon wannan shekara ta 2014 yawan bakin haure da suka samu nasarar shiga yankunan kasar Spain na Melilla da Ceuta ya karu. Biranen na Spain da ke arewa da kasar Marokko su ne kadai ke da iyaka ta kasa tsakanin Afirka da Turai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu