A cikin shekarar da ta gabata ta 2013 Tarayyar Turai ta taimaka wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da taimakon jinkai na kimanin Euro milyan 76. Daga cikin kwamitin kungiyar ya ba da Euro milyan 39 yayin da mambobin kasashe suka bayar da sauran kudaden.