Karin wuraren tarihi kan jerin na UNESCO
Taro na 44 na kwamitin kula da kayan tarihi na UNESCO, a birnin Fuzhou na kasar China, ya kara wasu sabbin wuraren tarihi kan wadanda hukumar ke da su.
Wurin shakatawa na Ivindo da ke Gabon
Ya kasance a yankin arewacin Gabon, wurin da akasarinsa gandun daji ne ya kai girman kusan kadada dubu 300 da ke kusa da kogin da ake kira "blackwater". Akwai ruwan da ke kwararowa daga tsaunuka a kan iyakar gandun dajin, hakan ya kara kawata kyaun wurin da kara darajarsa. Yanayin koramar wurin ya sa ana samun dabbobin ruwa.
Masallaci salon na Sudan a Cote d'Ivoire
Tsakanin karni na 17 da 19, 'yan kasuwa daga Sudan kan tafi fatauci har zuwa yankin yammacin Afirka. Ta haka ne aka samu cudanya tsakanin 'yan kasuwa da malaman Islama a Cote d'Ivoire. Yanzu an sanya masallatai 8 da aka gina da tabo cikin muhimman wuraren tarihi na duniya. Kuma sun kasance shaidar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, da ya taimaka wajen yada addinin Islama.
Wurin tarihi na Yahudawa na Jamus
Biranen Speyer da Worms da Mainz — da ke kusa da juna a gefen kogin Rhine — sun kasance cibiyar tarihin rayuwar Yahudawa a shekarun baya. Ana kiransu Shin da Vav da kuma Mem a harshen Hebrew na da, garuruwan uku gaba ɗaya ana kiransu biranen ShUM. Worms gida ne na makabartar Yahudawa mafi tsufa a Turai.
Nice, Faransa
Birnin Nice ya hade da sauran wuraren tarihin Faransa sama da 40 da suka hada da gabar kogin Seine da ke Paris da ginin majami'ar Amiens da Mont Saint Michel da kwarin Loire. Tarihin Nice da Bahar Rum da Alpine na Turai, ya samar da gine -gine da shimfidar wuri wanda babu kamarsa, abin koyi ga sauran biranen duniya.
Wuraren tarihi na Jomo da ke Japan
Wannan shi ne sansanin Sannai-Maruyama na kasar Japan, da ke dauke da baraguzai da sauran ginin matsugunnin 'yan Jomo. Ana tunanin wannan al'ada mai alaka da farauta ta kasance tun daga shekaru dubu 13 kafin haihuwar Annabi Isa, akalla na tsawon shekaru 300. A yanzu an sanya adadin wuraren tarihin na Jomo 17 cikin jerin wuraren tarihi na UNESCO.
Zanen dutsen Hima da ke Saudi Arabiya
Hotunan da aka samo a Hima sun ba da shaida ga al'adar rayuwar masu wadata a tsibirin Larabawar kimanin shekaru 7,000 da suka gabata. Hotunan dutsen da aka adana da kyau su na nuna yanayin farauta. Rubutun na cikin harsuna daban daban da suka hada da Larabci da Girkanci da Musnad, cikin tsohon takardar Larabawan kudanci. Yankin ya kasance kan tsohuwar hanyar da matafiya ke bi.
Tashar jiragen ruwan Guangzhou a Chaina
Tsohuwar tashar jiragen ruwa na Guangzhou — Mai binciken kasar Italiya Marco Polo ya taba ayyana ta a matsayin daya daga cikin wurare masu daraja da wadata a duniya — kuma an saka shi cikin jerin wuraren tarihi na UNESCO. Ya kasance a yankin gabar ruwa da ke gashin Chaina, wanda ya taka muhimmiyar rawa a kasuwanci ta cikin ruwa.
Wurin bauta na Ramappa a Indiya
Wurin bauta na Ramappa da ke Indiya, mai tazarar km 200 a yankin Arewa maso Gabashin Hyderabad, ya shiga cikin jerin wuraren tarihin hukumar UNESCO. A gina wurin ne da duwatsu a karni na 13. Ana masa kallon sa a matsayin daya daga cikin misalan muhimman wuraren tarihi na zamanin Kakatiyan.
Layin dogo mafi tsawo na Iran
An gina wannan layin dogo tsakanin shekarar 1927 zuwa 1938. Hanyar da tsawonta ya kai km 1,394 ta hada tekun Caspia da gabar tekun Persian, wadda ke alfahari da gadoji 360 da hannyoyin karkashin kasa 224. An yi mafi yawan aikin da kudaden harajin da al'umma ke biya, don kare tsoma baki daga ketare.
Sabbin layin ruwa na Dutch, a Netherlands
An tsara shi a matsayin fadada matakan tsaro, sabbin layin ruwan na Dutch sun bi ta cikin garuruwa 45 da yankuna shida da wuraren farauta daban daban da kuma ayyukan ruwa da fadinsa ya kai murabba'in KM 85. Ya yi aiki daga 1815 zuwa 1940, wanda ke da nufin kare makiya samun damar shiga Netherlands. A boye su ke ta yadda da wuya a gansu.