1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dawowar wasan damben gargajiya bayan hutun cilas na corona.

Gazali Abdou Tasawa AMA
June 22, 2020

Aksarin kungiyoyin Bundesliga sun san matsayinsu a daidai loakcin da ya rage wasa daya a kammala kakar wasannin ta shekarar bana. a Najeriya an sake komawa wasannin demben gargajiya bayan hutun cilas na Covid-19.

https://p.dw.com/p/3e9Ms
BdTD Nigeria | Dambe-Kämpfer
'Yan wasan dambe na dambacewa a wani gidan wasa na Abuja a NajeriyaHoto: Reuters/A. Sotunde

A wasannin Bundesliga tuni gishiri ya ji ma kan kaza duba da tebirin kakar wasannin domin kuwa bayan da tun a makonni da suka gabata kungiyar Bayern Munich ta lashe gasar Bundesligar a lokacin da ya rage wasanni uku a kammala kakar wasannin ta bana, daga nata bangare ita kuwa Borussia Dortmund mai maki 69 ita ma ta tabbatar da matsayinta na kasancewa ta biyu da ma samun tikitin shiga wasannin cin kofin zakarun Tutai, bayan da ta bi Leipzig har gida ta kuma doke ta da ci biyu da babu. Kuma sabon taurarin kwallon kafar nan na duniya wato Erling Haaland shi ne ya ci wa kungiyar Dortmund kwallayenta guda biyu. Kungiyar Mönchengladbach wacce ta bi Paderbon har gida ta kuma sarrafa ta da ci 3-1, ita ce kungiyar da ta fi cin moriyar wasanni na mako na 33 domin kuwa nasarar da ta samu ta ba ta damar kwace matsayi na hudu ga Leverkusen wacce ita ma ta yi raggonn kaya a Berlin a gaban Hertha inda ta doke ta da ci biyu da babu. Da makinta 62 Mönchengladbach na ma iya karbe matsayi na uku a tebirin na Bundesliga idan ta ci wasanta a gida a karawarta da Hertha Berlin idan kuma Leipzig mai maki 63 ta baras da wasanta na karshe da za ta buga a Ausburg. Sai dai ko ma mi zai faru leipzig za ta kasance daga cikin kungiyoyin hudu da za su wakilci Jamus a gasar Cin kofin zakarun Turai domin kuwa ba yadda za a yi Leverkusen mai maki 60 a yanzu ta kamu musamman sabili da yawan gwala-gwalen da Leipzig din take da. Sai dai akwai yiwuwar Kungiyar Leverkusen mai maki 60 ta iya karbe matsayi na hudu na shiga wasannin cin kofin zakarun Turai daga hannun Mönchengladbach idan a wasan na karshe ta yi nasarar doke Mainz ita kuma Mönchengladbach din ta kwata da kaya a gaban Hertha Berlin da ke iya jefa ta a matsayin ta biyar da zai jefa ta a wasannin Europa Ligue a maimakon na Champions Ligue. Ita ma dai Kungiyar Wolfsburg da ke a matsayin ta shida da maki 49 na iya samun tikitin shiga gasar Europa Ligue idan ta ci wasanta na karshe a gaban Bayern, amma kuma idan ta kuskura ta baras da wasan to kuwa Hoffenheim mai maki 49 ita ma na iya karbe mata matsayi idan ta yi nasara lashe wasanta a bakuncin da za ta kai a Dortmun. Idan muka koma a kasan tebirin na Bundesliga tuni baki alkalami ya bushe wa Kungiyar Paderbon wacce da makinta 20 kacal ta ciri tikitin komawa Bundesliga ta biyu a badi. A yanzu kungiyar da za ta yi rakkiyarta zuwa wannan rukuni Bundesliga ta biyu tsakanin Kungiyar Bremen mai maki 28 da Kuma Düsseldorf mai maki 30 shine ake dako, domin Idan dai har kungiyar Bremen da ke a matsayin ta 17 ta ci wasanta na karshe a gida a karawarta da Kolon, ita kuma Düsseldorf da ke a matsayin ta 16 ta baras da wasanta a gaban Union a birnin Berlin to kuwa za su rawar 'yan mata a tsakaninsu inda Düsseldorf za ta sauka ita kuma Bremen ta buga wasan ketarar saradi na Playoff. A takaice dai za a iya cewa a yayin da wasu kungiyoyin na Bundesliga suka riga suka san matsayinsu, a sama da kuma kasan tebirin wasu na jiran wasan karshe idan an an ne za ta kasance ko dai ta ware ko kuma ta wallare masu. Damben gargajiya ya sake dawowa

Nigeria Katsina | Traditionelles Boxen
'Yan damben gargajiya a NajeriyaHoto: DW/Y. Ibrahim Jargaba
Fußball Bundesliga Düsseldorf - Augsburg
'Yan wasan kungiyar Düsseldorf Hoto: Reuters/L. Kuegeler
Fußball Bundesliga 32. Spieltag - Leverkusen vs. 1. FC Köln
Leverkusen ta ci FC KölnHoto: Picture-alliance/AP Photo/I. Fassbender
Bundesliga Paderborn vs Mönchengladbach
Paderborn da MönchengladbachHoto: Getty Images/I. Fassbender

 Bayan kwashe fiye da watani uku da dakatar da wasan damben gargajiya a Najeriya, a yanzu an sake komawa a wasan damben a birnin Abuja hedikwatar Najeriya inda yanzu hakan komai ke tafiya daidai yadda ya kamata kamar yadda wakilin DW Hausa Uwais Abubakar Idriss ya ruwaito mana.