1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai dauki ga al'ummar Siriya

Yusuf Bala Nayaya
July 22, 2018

Dakarun sojan Isra'ila sun bayyana Lahadi cewa sun kwashi wasu daruruwan 'yan kasar Siriya da yawansu ya kai 800 da aka kai su zuwa wata kasa ta daban ba Isra'ila ba.

https://p.dw.com/p/31sOU
Flüchtlinge aus Daraa in den Golan-Höhen
Hoto: picture alliance/AA/A. Al Ali

A cewar Isra'ila ta yi wannan yunkuri ne saboda bukatar da Amirka da wasu kasashen Turai suka gabatar mata, abin da ke nuna cewa matakin ya zama na farko a tsawon shekaru bakwai na yakin basasar Siriya da Isra'ila ta yi irin wannan yunkuri na ba wa wasu 'yan Siriya dama su ratsa kasarta don neman guje wa yakin da kasar ke fama da shi.

A cewar sojan na Isra'ila dai an yi wannan aiki ne saboda dalilai na jinkai. Sai dai mai magana da yawun sojan na Isra'ila ta gaza tabbatar wa gidan jarida a Jamus na Bild labarin cewa wadanda aka kwashe din 'yan wata kungiyar agaji ce masu sanya fararen hula wadanda aka kwashe su zuwa Jodan.