Karshen fashin jirgin sama na Masar
March 29, 2016Talla
Sai dai kuma hukumomin na Cyprus sun sanar cewa karkata akalar jirgin ba ta da nasaba da ta'addanci, inda bayan wani lokaci ana tattaunawa mutumin ya fito daga jirgin hannayansa a sama kafin daga bisani jami'an tsaro su kama shi.
Jirgin kirar Airbus A-320 mai dauke da mutane 55 ya tashi daga birnin Alexandria zuwa Alkahira a kasar Masar kafin a karkata shi zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Larnaca da ke Kudancin tsibirin na Cyprus, inda mai magana da yawun fadar shugaban kasar Nikos Christodoulides ya ce wadanda aka tsare cikin jirgin na cikin koshin lafiya babu wani abu da ya same su.