1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi tir da tarzomar zanga zanga a G20

July 8, 2017

Taron G20 da aka kammala a birnin Hamburg ya kare ya bar baya da kura, inda zanga zangar lumana kan sauyin yanayi da manufar hadewar duniya wuri guda ta rikide zuwa tarzoma

https://p.dw.com/p/2gD8V
G20 Gipfel in Hamburg | Pfefferspray, Protest & Ausschreitungen
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Gateau

Zanga zangar dai ta daga hankalin musamman mazauna garuruwan Schanzenviertel da kuma Altona inda 'yan zanga zangar suka yi raga raga da kantuna da shaguna tare da kona motoci. 

Masu zanga zangar dai basu sami kaiwa harabar da aka gudanar da taron ba. Yan sanda kimanin dubu ashirin daga Jamus da kuma wasu kasashen turai suka bada kariya wajen tabbatar da tsaro a taron na Hamburg. Angela Merkel ta godewa 'yan sanda bisa gudunmawar da suka bayar na kange masu zanga zangar.

Deutschland, Hamburg, G20 Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

"Ta ce dukkan wadanda suka aikata wannan ba mutane ne masu kishin wanzuwar dimokradiyya da cigaban al'umma ba."
A jawabin bayan taro da shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar ta baiyana cewa daukacin kasashen 20 sun amince da matakan daidaita kasuwar hada hadar kudade da yaki da ta'addanci da kuma yakar halayyar kaucewa biyan haraji, wadanda suna daga cikin dalilan da suka jefa duniya cikin matsalar hada hadar kudade a shekarar 2008.
A waje guda dai taron bai cimma nasarorin da aka yi fatan zai samu na bai daya ba. Alal misali a fannin yaki da sauyin yanayi kasashe 19 sun jaddada goyon bayansu ga yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma da ake yiwa lakabi da "Paris Agreement a turance" Shugaban Amirka Donald Trump ya ki amincewa da matakin rage hayakin masana'antu a taron na Hamburg. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana matukar takaici da matakin Amirka kan wannan batu da ya hana cimma matsaya ta bai daya. Sai dai ta yi jinjina da yabo ga sauran gwamnatocin kasashe da suka amince da yarjejeniyar ta muhallin ta Paris.
"Ta ce ina godiya ga dukkan shugabannin kasashe da gwamnatoci da suka bada goyon baya ga yarjejeniyar kare muhalli ta Paris za mu tsaya babu ja da baya a kan wannan batu"

Deutschland Hamburg - G20 - Angela Merkel hält Rede
Hoto: Getty Images/AFP/K. Nietfeld
Deutschland Hamburg - G20 mit Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/AFP/J. Macdougall


A waje guda dai Shugaban Amirka Donald Trump ya baiyna aniyar cewa Amirka za ta aiwatar da samar da makamashi mai tsabta mara gurba yanayi. A game da batun cinikayya kuwa, kasashen na G20 sun cimma masalaha da kuma shawo kan jajajircewar Amirka na kare akidar cinikayyar kayan gida. A yanzu dai taron kolin ya amince da cinikayya ba tare da shamaki ba.