1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen ziyarar Rice a yankin gabas ta tsakiya

Zainab A MohammadOctober 5, 2006
https://p.dw.com/p/Btxs
Rice da Olmert a Izraela
Rice da Olmert a IzraelaHoto: AP

Kungiyar Nazarin ringingimu ta kasa da kasa,ta jaddada bukatar alummomin kasashen duniya su dada zage dantse wajen warware rikicin dake tsakanin Izraela da kasashen Larabawa.

Kungiyar nazarin ringimun tayi nuni dacewa yakin daya gudana tsakanin Izraela da yan Hizbollahi na Lebanon,na nuni dacewa idan ba mataki na gaggawa aka dauka wajen gano bakin zaren warware rikicin Larabawa da Izraelan tun daga tushe ba,matsaloli zasu cigaba da kunno kai babu kakkautawa.

Tace ya zamanto wajibi mdd da kungiyar Eu da kasashen larabawa baki daya ,su gabatar da sabon daftari adangane da halin taurin kai da izraela ke cigaba da nunawa,ayayinda dole uwargijiyarta watau Amurka ta fito fili ta nuna mata halin yakamata.

To sai dai kungiyar mai matsuguninta a birnin Brussels tace babu alamun zaa cimma wani tudun dafawa adangane da wannan batu,ganin yadda yankin na gabas ta tsakiya ke cigaba da dulmuyawa cikin rigingimu.

Ayanzu hakan dai yankin palasdinawa na fuskantar rigingimu na cikin gida ,da kuma halin da ake ciki a izraela bayan gwabzawa da Lebanon,da matsalolin rarrabuwar kawuna da gwamnatocin larabyawa ke fama dashi,ayayinda a bangare guda kuma rashin taka rawar gani a bangaren Amurka,wajwen warware ringinmun da suka dabaibaye yankin bamki daya.

To sai akarshen ziyarar aiki datake gudanarwa a yankin gabas ta tsakiya,sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta gaza cimma nasaran amincewar Izraela na rage matsin lamba da takeyiwa yankin palasdibnawa.

Jakadar Amurkan ta kammala wannan ziyarar wanzar da zaman lafiya a yankin larabawan ne ayau, ba tare da wata sanarwa adangane da ganawarta da takwararta Tzipi Livni da ministan tsaron izraela Amir Peretz ba.

Anyi zaton cewa Condoleeza Rice zata bada sanarwar nasara data samu adangane da matsin lamban da izraela takewa alummar palasinawa a kann iyakar zirin gaza,ziyarar da a hannu guda ke da nufin inganta dangantaka tsakanin shugaba Mahmoud Abbas mai sassaucin raayi,da kungiyar Hamas mai mulki a yankin palasdinawa.

To sai Sakatariyar harkokin wajen Amurkan tayi Alkawarin tallafawa,adangane da halin kuncin rayuwa da matsalolin na tattalin arziki da alummar palasdinawa ke ciki.

A liyafar cin abincinsu adaren jiya da premier Ehud Olmert na Izraela dai,Rice ta gaza shawo kanshi wajen sakin kudaden harajin da izraelan ke karba amadadin hukumar palasdinun ,wanda kasar yahudawa ke rike dasu tun kafin kungiyar hamas ta karbi ragamar mulki.Sai Dai Olmert yayi alkawarin gabatar da shawarwari adangane da yadda zasu tallafawa asibitoci,da magunguna a yankin na palasdinu.