180510 Südafrika WM Prostitution
June 10, 2010Sai dai kuma a yayinda a ɓangare guda wasu ke yin kiran gabatar da matakai na wayar da kai ga matan da ƙaddara ka iya rutsawa da su, a ɗaya ɓangaren kuma an samu masu yin kira da a halasta karuwancin domin fitar da matan daga ƙangin haramci.
Kimanin ɗalibai 15 ne suka hallara da sanyin wannan safiyar a cikin wani ɗan ƙaramin zaure na taro. Akasarinsu dai 'yan mata ne, waɗanda kuma su ne Bongiwe Mthethwa ta mayar da hankali kansu. Bongiwe dai ita ce shugabar wata ƙungiya ta matasan Afirka ta kudu da suka damu da makomarsu CYPSA a taƙaice kuma tun 'yan watanin da suka gabata take famar kai da komo a ƙoƙarin wayar da kan matasa game da haɗarin da zasu iya fuskanta lokacin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya. Kimanin tarurruka dubu ɗaya Bongiwe da takwarorinsa suka tasayar, musamman a makarantu, domin wayar da kan matasa a game da yadda za su iya kare kansu daga masu fataucin ɗan-Adam. An dai saurara daga Bongiwe Mthethwa tana mai bayanin cewar:
"Masu tilasta 'yan mata karuwanci kan kewaya loko-loko a duk faɗin ƙasar nan, musamman ma a yankunan karkara da wuraren da ake fama da talauci, inda su kan sace 'yan mata. Waɗannan 'yan mata suna fuskantar barazana, saboda ba zasu kasance a makaranta lokacin wasannin ba, zasu kasance ne a waje bakin tituna, lamarin da zai jefa su cikin mummunan haɗari. 'Ya'yanmu zasu fuskanci babbar barazana lokacin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya. Da dai muna da iko da mun kai so wani wuri a wajen Afirka ta Kudu."
Mahukuntan Afirka ta Kudu dai sun ƙiyasce cewar za'a samu ƙarin karuwai kimanin dubu 40, waɗanda za a tilasta su ayyukan lalata ba da son ransu ba. Amma a ɗaya ɓangaren masu goyan bayan karuwancin kamar ƙungiyar SWEAT dake garin Capetown sun ce an wuce gona da iri game da alƙaluman da aka bayar. Shi dai garin na Capetown mai tashar jiragen ruwa tuni ya zama wata cibiya ta karuwai. A sakamakon haka shugabar ƙungiyar ta SWEAT Vivienne Lalu ke yin kira ga hukuma da ta halasta karuwanci lokacin gasar ta cin kofin duniya, musamman ma ta la'akari da alƙaluman da aka bayar dangane da ƙwayar HIV a Afirka ta Kudu. Doka a ƙasar dai ta haramta karuwanci kuma ta tanadi hukunci na tara ko dauri a gidan kurkuku. Amma wannan haramcin na kawo cikas ga sa ido akan al'amuran kiwon lafiya a ƙasar, wadda ita ce ke da kashi ɗaya bisa biyar na masu ƙwayar HIV a duniya."
"A ganinmu kakkaɓe karuwancin daga zama wani babban laifi zai ba da wata kyakkyawar kafa ta ɗaukar matakan riga kafin kamuwa da ƙwayoyin cutar. Kazalika ta haka za a samu ikon tinkarar matsalar fataucin 'yan mata da ake yi. Akwai masu iƙirarin cewar mata kimanin dubu 40 aka shigar a Jamus lokacin gasa cin kofin duniya a shekara ta 2006, amma fa kawo yanzun babu wata shaida dake nuna hakan kai ko da ma mata biyar ne. A saboda haka nike ganin a nan Afirka Ta Kudun ma haka lamarin zai kasance."
Ita dai wannan ƙungiya ta SWEAT ba ta tsammanin samun goyan baya daga gwamnati akan manufarta, ballantana ma a kai ga canja dokar haramcin karuwancin a Afirka Ta Kudu.
Mawallafi: Ludger Schadomsky / Ahmed Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal