1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na kan gaba wajen karbar 'yan gudun hijira a Turai

Abdoulaye Mamane Amadou
December 24, 2022

Wasu bayanai daga hukumomi a nahiyar Turai sun tabbatar da Jamus ta samu karuwar adadin masu neman izinin zama a matsayin 'yan gudun hijira a wannan shekara.

https://p.dw.com/p/4LOKR
Deutschland | Landesamt für Einwanderung in Berlin
Hoto: Adam Berry/Getty Images

Wani rahoton da hukumomin shige da fice a nahiyar Turai suka fitar cikin sirri, ya ce Jamus ce kan gaba daga jerin kasashen nahiyar Turai da mutane suka fi neman izinin zama 'yan gudun hijira daga cikin kasashen nahiyar.

Jaridar Die Welt ta nan Jamus ta ce rahoton ya ce a wannan shekara ta 2022 mai karewa fiye da mutane dubu 190 ne suka shigar da takardun neman izinin zama a matsayinsu na 'yan gudun hijira a Jamus, adadin da ya karu da kaso 57 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar bara a daidai wannan lokaci.

Kasar Faransa na a matsayin ta biyu da ta samu karin adadin masu bukatar neman mafaka a wannan shekarar, sai kuma Spain da Ostiriya. Kasar Hangari ce kadai ta samu mafi kankanci na adadin mutane da ke bukatar mafakar, inda ta samu mutane 43 a wannan shekara.