Karuwar mata 'yan takara a kasar Lebanon
March 7, 2018Talla
Wannan shi ne karo na farko tun yau da shekaru tara da suka gabata da kasar ta Lebanon za ta gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a cewar kamfanin dillancin labaran kasar na ANI.
Akalla 'yan takara 976 ne za su nemi kujeru 128 na 'yan majalisar dokokin kasar, cikinsu mata 111. A zaben da ya gudana na shekara ta 2009, mata 'yan takara 12 ne kacal aka samu daga cikin 'yan takara 706 a tsakanin masu neman kujerar ta 'yan majalisa.
Majalisar dokokin kasar ta Lebanon ta yi ta kara wa kanta wa'adi har sau uku, sakamakon matsalar tsaro, da kuma rikicin siyasa da ke da nasaba da rikicin da ake a makwabciyata kasar Siriya.