Kasar Ethiopiya ta bude sabon babin zaman lafiya
November 3, 2022Manzon Kungiyar Tarayyar Afirka na musamman kuma tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaitar wuta a birnin Pretoria, bayan tattaunawar mako guda na bangarorin biyu a kasar Afirka ta Kudu. A jawabinsa Obasanjo ya ce: "Bangarori biyu a rikicin kasar Habasha sun amince a hukumance kan dakatar da fada da kuma shirin kwance damara cikin tsari da hadin kai da maido da doka da oda da barin a kai kayan agaji ba tare da cikas ba da kare fararen hula musamman mata da kananan yara da sauran rukunin mutane masu rauni".
Rikicin na Ethiopiya ya haddasa asarar rayuka da tagayyara jama'a daura da korar dubbai zuwa gudun hijira don tsira da rayukansu, inda suke ganin lokaci ya yi da za a bude sabon babi na zaman lafiya a wannan kasa da ke zama ta biyu mai mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Bangarorin biyu suka ce za su mutunta yarjejeniyar
Getachew Reda, babban mai shiga tsakani na Tigray ya ce : "An kashe mutanenmu ba kawai da bakin bindiga kawai ba, har ma da rashin abinci da magunguna. Yaranmu ba sa zuwa makaranta, kana asibitoci ba sa aiki saboda yaki. A koda yaushe muna kallo kamar an tilasta mana wannan yakin ne. A bangarenmu a shirye muke mu yi duk abin da za mu iya don dakatar da wannan yakin."
Masu shiga tsakani na Kungiyar Tarayyar Afirka sun danganta cimma yarjejejiyar da wani mataki mai muhimmanci na gina ingantaccen tubali na ceto martabar Ethiopiya da al'umarta, da kwance damarar yaki ba tare da bata lokaci ba, don rayuwa ta koma kamar yadda aka saba.
Redwan Hussein,e wakilin gwamnatin Habasha a tattaunawar ya ce: "Ya kamata dukkanmu mu mutunta wannan yarjejeniya, wajibi ne mu bi komai sau da kafa bisa ga tanadin wannan yarjejeniya. Al'ummar Habasha na da kyakkyawan zato fiye da tanadin yarjejeniyar. Suna bukatar zaman lafiya da jituwa, suna son ci gaba da muradin ingantacciyar makoma."
EU da Amirka da Jamus son nuna jin dadinsu kan yarjejeniya
A yayin da yake mika sakonsa na taya murna ga gwamnatin Ethiopiya da kungiyar TPLF, babban jami'in ketare na kungiyar Tarayyar Turai Joseph Borrell ya jaddada bukatar fara aiki da yarjejeniyar ba tare da bata lokaci ba. Kuma a maida fifiko kan bude kofofin shigar da kayan agaji a yankunan da yakin yafi shafa musamman Tigray. Kazalika Borrell ya karfafa musu gwiwar ci gaba da tattaunawar da za ta tabbatar dorewar yarjejeniyar zaman lafiya tare da kaddamar da tattaunawa kan siyasar kasar.
A nashi bangare, babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya kira yarjejeniyar da mataki mai sarkakiya na farko wajen kawo karshen yakin shekaru biyu da ya janyo wa Ethiopiya asarar rayuka masu dumbin yawa. Shi kuwa sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken yaba wa Kungiyar Tarayyar Afirka ya yi da wannan gagarumun mataki na cimma kwance damarar yaki. A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ministar harkokin waje ta Jamus Annalena Baerbock, ta ce cimma yarjejeniyar zaman lafiya na nufin wajibi ne ita ma Iritiriya ta ajiye makamanta kana ta janye mayakanta daga kan iyakokin Ethiopiya.
Shugabannin Afirka sun yi maraba da yarjejeniyar
Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu kuma shugaban Senegal Macky Sall da shugaba Williams Ruta na Kenya da ke makwabtaka sun yi maraba da cimma matsayar sulhu, inda shugabannin biyu suka jaddada ci gaba da bin matakin don ganin cewar an dawo da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al'ummar Ethiopiya. Tun a watan Nuwamban 2020 ne dai yaki ya barke tsakanin dakarun gwamnatin Ethiopiya da kungiyar TPLF, kuma ya zuwa yanzu Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta ce mutane miliyan biyar ne ke dogaro da tallafin abinci sakamakon wannan yakin.