Kasar Girka da masu ba ta bashi sun cimma matsaya
August 12, 2015Talla
Kasar Girka da masu ba ta bashi sun cimma matsaya kan shirin ceto tattalin arzikin kasar. Jami'ar kungiyar Tarayyar Turai mai magana kan tattalin arziki Annika Breidthardt ta tabbatar da haka, inda ta ce haka zai share hanyar ganawar ministocin kudin kasashen Turai masu amfanin da kudin bai daya na Euro zuwa ranar Jumma'a mai zuwa.
Karkashin sabon shirin Girka za ta samu kudaden da suka kai Euro milyan dubu-85, yayin da kasar za ta aiwatar da sauye-sauyen tayar da komadar tattalin arziki. Kasar Jamus ta ce za ta duba abin da shirin ya kunsa sannan ta fitar da matsaya zuwa karshen mako. Mai magana da yawun Shugabar Gwamnati Angela Angela Merkel ya tabbatar da cewa Merkel ta yi hira ta waya da Firaminista Alexis Tsipras na Girka sau biyu.