Girka ta gaza biyan IMF bashi
July 1, 2015Kasar Girka ta gaza a biyan bashi da kasashen Turai ke binta wanda cikar wa'adin da aka ba ta ya kammala a ranar Talata.
Asusun bada Lamuni na IMF ya tabbatar da cewa kasar ta Girka ta kasa biyan sama da miliyan dubu na Euro, abin zai sa babbar manajar asusun Christine Lagarde ta yi jawabi ga kasashen da suka biyo kasar ta Girka bashi.
Kasuwannin hada-hadar kudade dai sun shiga rudani ganin rashin biyan bashin na Girka zai iya sanya a cire ta daga cikin kasashe da ke amfani da kudin bai daya na Euro, sannan makomar kasar ta ci gaba da kasancewa mamba cikin kungiyar kasashen Turai ya dogara ga kuri'ar raba gardama da za a kada ranar biyar ga wannan wata na Yuli ko al'ummar kasar zasu zabi ci gaba da sanya musu sharuda na tsuke bakin aljihu ko kuma a a.