1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Iran ta saki 'yan Indiya da ta kama

Mouhamadou Awal Balarabe
July 26, 2019

Matuka jirgin ruwan Indiya da Iran ta kama a mashigin ruwa Hormuz makonni biyun da suka wuce sun samu kansu. Sai dai ba a bayyana dalilan sakesu ba duk da takun saka tsakanin Iran da Amirka da Birtaniya kan nukiliya.

https://p.dw.com/p/3MmfH
Iran | Britischer Tanker Stena Impero | Iranische Revolutionsgarde
Hoto: picture-alliance/abaca

Kasar Iran ta saki mutune tara daga cikin ma'aikatan jirgin ruwan Indiya 12 da ta kama a ranar 14 ga wannan wata na Yuli bisa zargin safarar man fetur ta hanyar da ba ta dace ba. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Indiya ce ta bada sanarwa ba tare da cikakken bayani kan hanyoyin da aka bi wajen sakin ma'aikatan ba. Fadar mulki ta Teheran ta kame jiragen ruwan da dama da ke shiga kasarta biyo bayan takun saka tsakaninta da Ingila da kuma Amirka kan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin ruwan Hormuz.

Wani shafin yanar gizo na TankerTrackers da ke bin diddigin jigilar jiragen ruwa ne ya ruwaito kwanaki 12 da suka gabata cewa jirgin da ake yi wa lakabi da MT Riah ya shiga cikin ruwan Iran, kuma  ya daina jin duriyarsa daga bisani. A halin yanzu dai kasar ta Iran na ci gaba da rike wasu Indiya 21 ciki har da matuka jirgin MT Riah da kuma wasu karin 18 wadanda sojoji suka kame a makon da ya gabata.