1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Ukraine na bikin samun 'yancin kai

August 24, 2022

Yayin da Ukraine ke fama da yaki da Rasha ta kaddamar a kanta yau watanni shida cur, kasar na bikin samun 'yancin kai inda take cika shekaru 31 da zama mai cikakken iko.

https://p.dw.com/p/4FwtT
Ukraine-Krieg | Tag der Nationalflagge in Uschgorod
Hoto: Serhii Hudak/Avalon/Photoshot/picture alliance

Shugaban kasar ta Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana ranar ta 'yanci a matsayin muhimmiya, yana mai farin cikin cewa kan 'yan kasar a hade yake kuma suna magana da murya guda.

Sai dai shugaban na Ukraine ya bayyana fargabar yiwuwar Rasha ta iya daukar mataki mai muni a kan kasar a wannan rana da take matukar girmamawa.

Shugaba Zelenskyy ya ce Rasha na iya far wa Kyiv babban birnin kasar da ma sauran wasu manyan biranen a wannan rana.

Gwamnati ta ma ayyana dokar hana zirga-zirga a wannan rana ta 'yanci a Ukraine, inda Shugaba Zelenskyy ke kira ga 'yan kasar da su tabbatar da bin doka, tare da kasancewa cikin yanayi na takatsantsan.