1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabin matakai bayan harin cibiyar G5 Sahel

Salissou Boukari
June 30, 2018

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da na kasar Kamaru Paul Biya sun yi Allah wadai da harin kunar bakin waken da aka kaiwa cibiyar ma'aikatar rundunar tsaro ta G5 Sahel da ke birnin Sévaré a kasar Mali.

https://p.dw.com/p/30bTv
Mali, Sevare:  G5 Sahel force's Militärstützpunkt / Symbolbild
Hoto: Reuters/A. Ross

Wannan hari da tuni kungiyar 'yan jihadi ta yankin na Sahel ta dauki alhakin kaiwa, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, kuma ya wakana ne kwanaki uku kacal kafin ziyarar da shugaban kasar ta Faransa zai kai a Afirka, inda zai halarci taron kungiyar Tarayyar Afirka da zai gudana a kasar Mauritaniya. Shi ma daga na shi bangare ministan harkokin wajen kasar Mauritaniya Ismail Ould Cheikh Ahmed ya ce batun yakar 'yan jihadi yanzu ma suka soma: 

" Abun da ya wakana a jiya mun yi Allah wadai da shi kuma hakan na nuni da mahimmancin da wannan tunani da shugabannin kasashen na G5 Sahel suka yi kuma hakan ba zai sa mu yi kasa a gwiwa ba."

Shugaban na Faransa zai gana da shugabannin kungiyar ta G5 Sahel a daura da taron na Tarayyar Afirka. Yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, shugaban na Faransa da na Kamaru sun kuma tabo batun matsalar tsaro a yankin tafkin Chadi da kuma mahimmancin ci gaba da hulda tsakanin kasashen yankin wajen yakar 'yan ta'adda.