Kasashe na ci gaba da neman sulhunta Isra'ila da Hamas
March 22, 2024Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa birnin Tel Aviv na kasar Isra'ila domin jaddada bukatar kai karin agajin jinkai ga Zirin Gaza, a daidai lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gabatar da kuduri na tsagaita bude wuta a yankin na Falasdinu.
Fadar mulki ta Washington na neman shawo kan kawayarta Isra'ila don ta kauce ma kai farmaki ta kasa kan garin Rafah da ake fargabar karuwar 'yunwa tsakanin fararen hula.
Kasar Burtaniya da ke zama mamba ta din din din a kwamitin sulhu da kuma kasar Ostireliya sun yi kira da a gaggauta kawo karshen yakin da aka shafe watanni biyar da rabi ana yi a zirin Gaza, domin ba da damar isar da kayan agaji da kuma sako 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa bayan da Hamas ta kai mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoba.
A gefe guda yayin da jami'an diflomasiyya ke cikin matsin lamba, ana ci gaba da gwabza fada a ciki da wajen asibitin al-Chifa, inda sojojin Isra'ila suka yi ikirarin kashe Falasdinawa sama da 150.