Kasashen Afirka na kokarin fadada arzikinsu
November 25, 2022Shugabannin kasashe da na gwamnatoci Afirka kimanin 15 ne suka halarci taron kungiyar ZLECAF na birnin Yamai domin nazarin hanyoyin bunkasa masana'antu a nahiyar ta yadda kasashen za su fi amfanar juna a fannin cinikayya da kuma taka rawa a harkokin kasuwanci a duniya. Da yake jawabi lokacin bude taron, shugaban kwamitin gudanarwa na Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat ya bayyana takaicin irin yadda duk matakan bunkasa masana'antu da Afirka ta dauka a baya suka kasa kai labari.
To sai dai Madame Aissata Sall, ministar harkokin wajen kasar Senegal da ta wakilci Shugaba Macky Sall, wanda shi ne shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU a wajen wannan taro, tunatarwa ta yi na irin arzikin da Allah ya huwace wa nahiyar ta Afirka wanda za ta iya dogaro da shi wajen gina masana'antu.
A nashi bangaren Shugaba Mouhamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar, ya ce idan har yanzu Afirka na son cimma burinta na bunkasa masana'antunta da tattalin arzikinta, ya zama dole ‘yan nahiyar su fada wa juna gaskiya. A cewarsa Afirka na da kaso hudu cikin dari a kasuwancin duniya. Sannan kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar duka-duka kaso 17 ne cikin dari.
Ya ba da misalin ce Nijar wacce ke daga cikin kasashen Afirka da suka fi arzikin dabbobi, abin takaici sai ka ga suna yiwo odar madara daga kasashen Faransa da Holland. Makwabtan Nijar kuma na yiwo odar nama daga kasashen Ajentina da New Zeland, lamarin da ke cutar da makiyayan Afirka da kuma tauye shirinsu na bunkasa masana’antun a kasashenmu
Abin jira a gani dai a nan shi ne tasirin da shawarwarin da taron na shugabannin kasashen Afirka na birnin Yamai za su yi wajen bunkasa masana'atu da da shawo kan matsalolin da ke kawo tarnaki wajen aikin da yarjejeniyar kasuwancin maras shin ta Zlecaf shekaru uku ba