SiyasaJamus
Kasashen Afirka sun ceto kansu a MDD
January 21, 2021Talla
Mai magana da yawun Malajisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya ce kasashen uku na nahiyar Afirka sun biya basukan ne bayan dakatar da su da aka yi a makon jiya, koda yake bai bayyana adadin kudaden ba.
Sai dai ta bayyana cewar kasar Libiya ta biya dala dubu bakwai da biyar da 391 yayin da Nijar ta biya dala dubu shida da 733, sai kuma kasar Zimbabuwe da ta mika dala dubu 81 da 770.
Har yanzu akwai kasashe irin su Iran da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Kwango Brazaville da ma Sudan ta Kudu, wadanda duk Majalisar Dinkin Duniyar ta dakatar saboda rashin sauke nauyin da ke a kansu na rance.