Kasashen Amirka da Iran na zama kan nukiliyar Iran
March 16, 2015Tattaunawa kan batun makamashin nukiliyar Iran, ta shiga wani muhimmin gaba a wannan Litinin, kasancewar Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry zai gana da takwaransa na Iran Mohammad Zarrif a birnin Lausanne na kasar Switzerland, domin cimma matsaya ta kwarai dangane da batun da a yanzu aka dauki watanni 18 ana tattaunawa kansa.
Yayin da lokaci ke kara matsowa, ana sa ran manyan jami'an kasashen biyu za su tattauna abin kirki a zaman da suke yi a Switzerland, wanda bayansa ne ake fatan kammala komi ranar 1 ga watan Yulin bana.
John Kerry Amirka tare da Mohammad Zarrif na Iran din dai, na fuskantar matsi daga wasu al'umomi a cikin gida, wadanda ke ganin akwai bukatar tsayuwar kasashen kan batun na nukiliya.
Tun farko dai Mista Kerry ya fada a kasar Masar gabanin kama hanyarsa ta zuwa Switzerland din, cewar burinsu dai shi ne cimma matsaya, matsaya kuwa ta hakika.