Kasashen dake amfani da Euro
December 4, 2011Kasashe nawa ke amfani Euro?
Baki daya a halin da ake ciki yanzu kasashe 17 ke amfani da takardar kudi ta Euro.
A shekara ta 2002 aka fara amfani da Euro.
Amma tun 1999 ,kasashe 11 suka cimma yarajejeniyar amfani da wannan kudi, kasashen kuwa sune Jamus, Faransa, Austriya,Beljiam,Spain,Finland,Irland,Luxemburg,Holland, Italiya da Portugal.
Daga bisani sauran kasashe suka biyo baya, Girka ta shiga a shekara 2001, Sloveniya a shekara 2007, tsibirin Malta da Siprus a 2008, Slovakiya ta shiga a shekara 2009.
Kasa ta baya-bayan nan wadda ta shiga Euro itace Estoniya a farkon shekara 2011.
Saidai yanzu haka akwai kasashe da dama na Turai masu zawarcin samun matsayin memba a cikin rukunin masu amfani da Euro, duk kuwa da matsalolin tattalin arziki da wannan kasashe ke fama da su.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal