1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goyon bayan kasashen duniya kan kafuwar kasar Falasdinu

Mahmud Yaya Azare MNA
January 16, 2017

Matakin da kasashen suka dauka a taron neman zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu a birnin Paris, ya jawo mai da martani daga masu ruwa da tsaki kan rikicin.

https://p.dw.com/p/2VrRs
Paris Nahost Konferenz
Hoto: Getty Images/AFP/B. Guay

Taron da shi ne na biyu da Faransa ta dauki dawainiyar shiryawa cikin kasa da shekara guda, wanda bangarorin da ke rikicin, wato Isra'ila da Falasdinawa suka kaurace masa, ya samu halattar wakilan kasashe 75 wadanda bakinsu ya zo daya kan adawa da ci gaba da gina matsugunan share wuri zauna da Isra'ila ke yi a yankunan Falasdinawa. Mahalarta taron sun kuma jaddada goyan bayansu ga kafuwar kasar Falasdinu mai cikakkyen 'yanci, amman fa ta hanyar tattaunawa kai tsaye tsakanin Falasdinawa da Isra'ila, inji mai masaukin baki a taron shugaban Faransa Francois Hollande.

"Kudurin da muka yi ammanar zai samar da dauwamammen zaman lafiya, shi ne samuwar kasashe biyu masu 'yanci ta hanyar tattaunawa kai tsaye tsakanin Isra'ila da Falasdinawa. Ba wanda zai yi haka a madadinsu."

Firaministan Isra'la Benjamin Natenyahu, wanda ya soki taron, ya ce babu abun da zai tsinana in banda kawo tsaiko ga tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da Falasdinawa.

"Wannan taro na Faransa shakulatun bangaro ne. Taro ne na ziga Falasdinawa su kara bijirewa, lamarin da zai nesantasu da tattaunawar da za ta amfanar da su. Wannan taro shure-shuren mutuwa ne ga tsohon tsarin duniya."

Taron Paris ya sha yabo daga Falasdinawa

Mahmud Abbas und Benjamin Netanjahu bei Nahost-Friedensgesprächen
Mahmud Abbas da Benjamin Netanyahu sun samu bambamcin ra'ayi game da taronHoto: picture-alliance/dpa

Falasdinawa da suka yi maraba da sakamakon taron, sun ce ko ba komai, taron wata manuniya ce ga yadda Isra'la ke kara mai da kanta saniyar ware a duniya. Muhammad Shatiyyah kusa ne a hukumar Falasdinawa da ya ce:

"Taron Faransa taron dangin kasashen duniya ne don tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen mamaya. Sukan da Isra'la ke wa irin wadannan taruka, na nuna yadda sannu sannu take fitar da kanta daga dangi."

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da zaman tankiya ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon zakewar da Isra'ila ke yi wajen fadada matsugunan share wuri zauna a yankunan Falasdinawa. Taron ya kuma zo ne kasa da kwanaki biyar kafin sabo Shugaban Amurka Donald Trump ya kama aiki, wanda ya jima yanashan alwashin sauya wa ofishin jakadancin Amurka a Isra'la mazauni daga Tel Aviv zuwa Brnin Kudus da zarar ya dare kan karagar mulki, lamarin da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce "idan har ya tabbata, to Falasdinawa za su yi watsi da halaccin kafuwar kasar Isra'la baki daya", matakin da tabbas zai kara dagula lamura a yanki.