Kasashen duniya na juyayin mutuwar Pele
December 29, 2022Bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu ta Ingila a watan Satumba, Pele ya zama wani babban jigo na karni na 20 da ya riga mu gidan gaskiya, lamarin da ya haifar da martani daga duniyar kwallon kafa da kuma ta siyasa. Tun daga shugaban kasar Amirka Joe Biden har zuwa taurarin kwallon kafa irinsu Neymar ko Kyllian Mbappé, duk sun karrama Pelé da ke zama tauraron kwallon kafa na farko a duniya, wanda cutar kansar hanji ta yi ajalinsa yana da shekaru 82 a duniya. Sanarwar mutuwar Pelé, wanda ainihin sunansa Edson Arantes do Nascimento ta girgiza shugabannin duniya, lamarin da ya sa su nuna alhininsu a kafoffin sada zumunta.
Shugaba Joe Biden na Amirka ya wallafa a shafinsa na twitter daga fadar White House cewa "tarihin Pelé a fagen kwallon kafa tun daga farkon zuwa matakin kololuwa ya nuna cewa komai mai yiwuwa ne. Shi kuwa zababben shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva cewa ya yi: ba a taba samun lamba 10 kamarsa ba.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Michel Platini da Zinedine Zidane da Cristiano Ronaldo na Portugal sun wallafa hotunan da suka dauka a baya a marigayi Pele tare da bayyana shi a matsayin "mafi girma da daraja" daga 'yan wasan kwallon kafa a duniya.
A nasa bangaren, shugaban kasar Brazil mai barin gado Jair Bolsonaro, ya yaba tare da girmama wanda ya kira "mutumin da ya daukaka sunan kasar a duniya.
Shi ma shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya mika sakon ta'aziyyarsa ga takwaransa na Brazil bisa rasuwar Pelé, wanda ya danganta da "babban mutum" kuma "abin alfaharin Brazil", a cikin wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar. Shi ma Gianni Infantino da ke zama shugaban FIFA ba a bar shi a baya ba wajen jajanta rasuwar Pele.
Duniyar wasanni na sahun gaba wajen juyayin rashin tsohon dan wasan kwallon kafa na Brazil Pele, wanda ya zama daya tilo da ya taba lashe kofin duniya sau uku a tarihi. Hasali ma 'yan wasa da alkalan wasan Premier League ta Ingila su sanya bakaken kyalle a hannu, sannan suka tafa na minti daya a matsayin karrama Pele, kafin a fara karawa tsakanin Liverpool-Leicester da West Ham-Brentford a wasannin mako na 18.
A Italiya ma, za a yi shiru na minti daya a filayen wasa yayin da za a fagen wasanni bayan hutun a gasar Seria A a ranar 4 ga Janairu, in ji hukumar kwallon kafar kasar. A Spain, LaLiga ta sanar cewa za a yi shiru na minti daya kafin kowane wasa na mako na 15 na gasar. haka ita ma Faransa ba a barta a baya wajen daukar irin wannan mataki ba.
Akwai 'yan wasan kwallon kafa da dama da kuma shugabannin hukumomin kasashen Afirka da suka mika sakon ta'aziyarsu bayan mutuwar Pele. Augustin Senghor, daya daga cikin mataimakan shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Senegal, ya tuna rangadin da sarki Pelé ya kai a Dakar da kungiyarsa ta FC Santos.
Ko da shi ma shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijar Djibrilla Hima Hamidou irin wannan lakabi na Pele ya yi ta amfani da shi. A gare shi, Sarki Pelé shi ne cikakken dan wasan kwallon kafa da ya zarta sa'a, kuma abin koyi. Sarki Pelé ya kasance madogarar farko ta karfafa gwiwa ga 'yan wasan kwallon kafa da yawa a nahiyar Afirka.
Pele ya mutu ne a ranar Alhamis yana da shekaru 82 da haihuwa sakamakon cutar kansa ta hanji. A ranar Talata ne za a binne Pele bayan shafe yinin litinin ana karrama gawarsa tare da bai wa 'yan Brazil damar yin ban kwana da shi.