Kasashen duniya na kira da a kawo karshen yakin Gaza
August 9, 2024Talla
A wannan Alhamis, ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ta amince da ci gaba da tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza daga ranar 15 ga watan Agusta bisa bukatar masu shiga tsakani na Amurka da Qatar da kuma Masar.
Masu shiga tsakani na Amurka da Qatar da Masar sun yi kokarin tabbatar da sulhu na biyu a yakin da aka shafe watanni 10 ana yi, sakamakon harin da Hamas ta kai wa Isra'ila wanda ba a taba ganin irinsa ba a ranar 7 ga watan Oktoba.
Rikicin da ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar kashe dubban mutane, daura da hali na tagayyara, da yaduwar cututtuka tsakanin mazauna Gaza da ke neman mafaka daga hare haren Isra'ila babu kakkautawa.