1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun cire wa Iran takunkumi

Gazali Abdou TasawaJanuary 17, 2016

Hukumar Kula da Makamashin Nukliya ta Duniya IAEA ta ce kasar ta Iran ta mutunta illahirin sharudan da aka gindaya mata lokacin saka hannu kan yarjejeniyar nukiliya

https://p.dw.com/p/1HerO
Österreich Wien Atomverhandlungen USA Iran IAEA
Hoto: Reuters/L. Foeger

Hukumar Makamashin Nukliya ta Duniya ta bada na'am dinta ga soma aiki tun a ranar Asabar da yarjejeniyar nukliyar da kasar Iran ta cimma da manyan kasashen duniya a cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.

Hukumar ta ce kasar ta Iran ta mutunta illahirin sharudan da aka gindaya mata lokacin saka hannu kan yarjejeniyar.Tuni kuma manyan kasashen duniyar suka soma bayyana gamsuwarsu a kai.

Firaministan kasar Burtaniya John Kerry Kenan ya ce bayan tattauanwa ta sama da shekaru biyu da rabi ,Hukumar Makamashin Nukliya ta Duniya ta tabbatar da cewa Iran ta mutunta alkawarinta na kwance damarar shirinta na neman kera makamin nukiliya kamar dai yadda yarjejeniyar da ak cimma da ita a watan Julin ta tanada

Tuni dai manayan kasashen duniya suka soma bayyana matakin dage jerin takunkuman tattalin arzikin da suka sakawa kasar ta Iran kamar dai yadda dama yarjejeniyar ta tanada.

Kungiyar Tarayyara Turai wacce tuni ita ma ta dauki matakin dage takunkumin ta ce za ta tabbatar da shi ta hanyar wallafa kudirin dokar da ta dauka kan batun a cikin jaridar wallafa dokokinta a kwanaki masu zuwa.