Kasashen EU za su taro a kusa da Ukraine
June 1, 2023Talla
Taron dai ya kunshi dukannin kasashe mambobi 27 na kungiyar tarayyar Turai da kuma wasu kasashen Turan. Manufar taron ita ce, nuna goyon baya ga kasashen biyu yayin da Ukraine ke shirin mayar da martani ga mamayar da Rasha ta kaddamar a kasar. Taron na wannan Alhamis din wanda ba gayyaci kasashen Rasha da Belarus ba na kasancewa bita kan taron da shugabannin suka gudanar a bara a birnin Prague domin tattauna kalubalen siyasa.
A lokacin da take ganawa da manema labarai, shugabar kasar Maldova Maia Sandu ta ce zuwan shugabannin ya nuna cewa ana tare da Moldova da kuma makwafciyarta Ukraine, wadda ke fuskantar mamayar Rasha. Ana sa ran shugaban Ukraine Volodmyr Zelenskyy ya halarci taron.