1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G5 Sahel ta jaddada kudirinta kan tsaro

Gazali Abdou Tasawa
September 26, 2019

Shugabannin kasashen Afirka mambobin Kungiyar G5 Sahel sun jaddada wa Majalisar Dinkin Duniya bukatar ganin ta dauki nauyin kudaden tafiyar da ayyukan kungiyar na yaki da ta‘addanci.

https://p.dw.com/p/3QIVe
USA Greta Thunberg in NewYork
Greta Thunberg deltar på FN klimat toppmöte för unga i...
Hoto: picture-alliance/TT NYHETSBYRÅN/P. Lundahl

Kasashen sun bayyana wannan bukata ce  a jawabin da suka gabatar a taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Sai dai wasu masana a nahiyar na ganin hanyar da shugabannin G5 Sahel ke bi wajen shawo kan matsalar tsaron yankin ba mai bullewa ba ce.

Shugabannin na G5 Sahel sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasafin kudin kungiyar a babi na bakwai na dokar tsarin aikin Majalisar Dinkin Duniyar wanda ya halitta wa majalisar daukar matakan tunkarar duk wata matsala da ke barazana ga zaman lafiyar a kowane yanki na duniya.

Da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniyar Shugaban kasar burkina Faso kana shugaban kungiyar ta G5 Sahel Rock Marc Christian Kabore ya bayyana matsalar kudin tafiyar da aiki da kungiyar take fuskanta musamman yadda kasashen duniya suka kasa cika alkawarran tattafin kudi da suka yi wa kungiyar

African Union summit
Shugaban Burkina Faso kuma shugaban G5 SahelHoto: Getty Images/I. Sanogo

"Muna jaddada bukatar ganin an dauki nauyin rundunar G5 Sahel a karkashin kasafin Majalisar Dinkin Duniya, ta yadda za ta samu kudaden aiki na dindindin. Idan aka samar wa rundunar da kayan aiki, aka karfafa aikin rundunar MINUSMA da sauran rundunoni na sauran kawayenmu, to ba shakka za mu iya tunkarar barazanar ta'addanci a yankin Sahel"

To sai dai Ahmed Ould Abdallah tsohon mataimakin babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya na ganin hanyar da kasashen na G5 Sahel ke bi tun farkon kafuwar kungiyar ba mai bullewa ba ce, kuma yankin ba zai rabu da matsalar ta’addanci ba, matukar kasashen ba su dauki matakan shawo kan matsalar da kansu ba.

Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey
Wasu shugabannin na kungiyar G5 SahelHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Hanya mafi a'ala ta yakar ta'addanci da ma duk wani abokin gaba shi ne samun gagarumin hadin kai tsakanin kasashen na Sahel. Domin a yau akwai sojoji kimanin dubu 30 a yankin. Idan har kasashen ba su iya dagewa ga fito da kudaden samar da kayan aiki ga sojojinsu ba, ko Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyin rundunar babu wani sauyi da za a samu."

Su kuwa daga nasu bangare shugabannin kasashen Nijar, Mali da na Chadi bayyana wa taron Majalisar Dinkin Duniyar suka yi cewa yanayin yakin da kasar Libiya ke fama da shi, na shafar yanayin tsaron kasashensu kai tsaye. Kuma suka ce nauyi ya rataya ga kasashen Turai da Amirka wadanda suka haddasa wannan yaki su gaggauta daukar matakan kashe wutar wannan rikici.