1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Gulf na son a rufe Al-Jazeera

Ahmed Salisu
June 23, 2017

Kasashen nan 4 na yankin Gulf da suka yanke huldar jakadanci da Qatar saboda zarginta da tallafawa aiyyukan ta'addanci sun mika mata jerin bukatu 13 kafin su daidaita ciki kuwa har da rufe gidan talabijin din Al-Jazeera.

https://p.dw.com/p/2fE9W
Symbolbild - Al-Dschasira
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Ulmer

Rage hulda tsakanin da Iran ma na daga cikin bukatun a kasashen na Gulf suka gabatarwa Qatar dun, har wa yau kuma kasashen na son ganin Qatar din ta rufe sansanin sojin Turkiyya da ke kasarta. Baya ga wannan, kasashen wanda suka hada da Saudiyya da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar na son ganin kasar ta Qatar ta yanke duk wata hulda da kungiyoyin da suka hada da Muslim Brotherhood da Hezbollah da IS da Jabhat Fateh al Sham da makamantansu. A cikin kwanaki goman da ke tafe ne dai wadannan kasashe da ke zaman doya da manja da Qatar din suke son mahukuntan na Doha su kai ga cika wadannan sharudda da suka gindaya muddin suna son ganin an warware wannan takun saka da ke tsakaninsu.